in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama wani da ake zargin mai hadawa Boko Haram bam ne a Nijeriya
2018-04-11 09:57:34 cri

Runduanr sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa, dakarunta sun cafke wani da ake zargin dan ta'adda ne, wanda ya kware wajen hada bam ga kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Onyema Nwachukwu ya fitar jiya Talata, ta ce an kama mutumin mai suna Adamu Hassan ne a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Nijeriya, biyo bayan wani samame da dakarun da kuma 'yan sandan farin kaya suka kai da yammacin ranar Litinin da ta gabata.

A cewar sanarwar, har ila yau a wannan rana, dakarun sun kuma cafke wasu mayakan Boko Haram da suka farwa wani yanki a yunkurinsu na neman abinci.

Kakakin rundunar ya ce, tuni mai hada bam din da sauran wadanda aka cafke suka tabbatar da ayyukansu ga jami'an tsaro. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China