in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a Habasha ya yi karin haske game da gurguwar fahimtar mu'amalar Sin da Habasha
2018-06-11 09:24:57 cri

Jakadan kasar Sin a Habasha Tan Jian ya fada a jiya Lahadi cewa, rashin fahimtar da wasu ke da shi game da yadda kasar Sin ke hulda da Habasha ba shi ne ainihin abin da yake a zahiri ba.

Jakada Tan Jian, wanda ya bayyana cewa yadda wasu ke bayyana ra'ayoyi marasa kyau wajen rage kimar jarin da kasar Sin ta zuba a kasar ta gabashin Afrika, babu kamshin gaskiya game da rahotannin.

Game da batun cikakken tsarin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, Tan ya ce, jarin da kasar Sin ta zuba a Habasha ya ninka a shekarar 2017 idan aka kwatanta da adadin na shekarar 2015.

Tan ya yi wannan tsokaci ne a lokacin kaddamar da katafaren kamfanin hada magunguna na kasar Sin wato Sansheng Pharmaceuticals Plc, wanda ya fara aiki a kasar ta gabashin Afrika a jiya Lahadi.

A cewar Tan, ingancin magungunan na kamfanin da sauran kamfanonin kasar Sin dake Habasha, game da matsayin fasahohin da suke amfani da su, za su iya yin gogayya da na kasashen da suka ci gaba.

Tan ya ce, mu'amalar kasar Sin da Habasha ta shafi zuba jari ne, da bunkasa masana'antu, da ci gaban kayayyakin more rayuwa, wanda ya bayyana su da cewa, su ne manyan abubuwan da kasar Habasha da sauran kasashen Afrika suke bukata don samun ci gaba.

Duk da irin gurguwar fahimtar da wasu ke nunawa, gwamnatin kasar Sin a shirye take ta ci gaba da yin hadin gwiwa da Habasha, kuma a hakika tana da tabbacin samun kyakkyawar makoma ga Habasha. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China