in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan yi wa tsarin hukumar WTO garambawul
2018-11-24 15:48:30 cri

Ma'aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar tana goyon bayan yi wa tsarin hukumar kula da harkokin cinikayya ta duniya wato WTO garambawul.

A cewar mataimakin ministan ma'aikatar Wang Shouwen, huldar kasa da kasa na fuskantar barazana daga daukar ra'ayi na kashin kai da kariyar cinikayya, a don haka, ya ce kasar Sin na goyon bayan sauya tsarin hukumar WTO, ta yadda zai kara karfi da inganci.

Ya ce, ya kamata sauya tsarin WTO ya bi muhimman ka'idoji 3 da suka hada da: daukaka ka'idar hukumar ta tabbatar da daidaito da bude kofa, da kare muradun ci gaba na kasashe masu tasowa mambobin kungiyar da magance wahalhalun da suke fuskanta dangane da batun dunkulewar tattalin arzikin duniya da kuma daukar matakin yanke kuduri bisa cimma matsaya guda daga bangarori daban daban.

Har ila yau, ya ce ya kamata sauyin ya daukaka matsayin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da mayar da hankali ga magance batutuwan dake barazana ga kasancewar hukumar da kyautata ka'idojin cinikayya, ta yadda za su dace da bukatu na zamani da tabbatar da ba da kulawa ta musammam ga kasashe masu tasowa, da kuma martaba tsarin neman ci gaba na kowacce mamba.

Wang Shouwen, ya ce kasar Sin na adawa da matakin wani bangare guda na rainawa da kin yarda da tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, yana mai gargadin cewa, daukar ra'ayi na kashin kai na barazana ga ka'idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China