Darakta janar na hukumar ciniki ta duniya WTO Roberto Azevedo, ya ce, harkokin cinikayya na duniya suna fuskantar matsin lamba, sai dai ba'a sani ba ko wannan halin da ke ciki yakin ciniki ne da ake yi, amma ya bukaci a dauki matakai.
Wata kidddigar WTO ta nuna yadda aka samu sauye sauyen al'amurra cikin watanni 6.
Yanayin da ake ciki zai iya yin tasiri kan tattalin arziki, da yin barazana ga ayyukan yi a dukkan kasashen duniya, inda lamarin zai fi jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali, in ji Azevedo.
Azevedo ya ce, dukkanin kasa da kasa suna da rawar da za su taka wajen warware matsalar.(Ahmad Fagam)