in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in WTO ya bukaci a karfafa tsarin hukumar don ci gaban duniya
2018-07-26 16:13:04 cri

Darakta janar na kungiyar ciniki ta duniya WTO Roberto Azevedo, ya yi gargadin cewa, karuwar kafa shinge a tsarin cinikayya zai iya zama wata sabuwar al'ada a bisa tsarin ciniki na kasa da kasa a lokuta masu zuwa a nan gaba, inda ya bukaci a karfafa tsarin kungiyar WTO da ake amfani da su a halin yanzu don tabbatar da samun bunkasuwar duniya.

A taron manema labarai da aka gudanar, Azevedo ya ce, wani rahoto na baya bayan nan da WTO ta fitar ya nuna cewa, daga watan Oktoban bara zuwa watan Mayun bana, shigayen da aka sanya a harkokin ciniki a fadin duniya, wadanda suka hada da sanya haraji da tsaurara ka'idojin hukumar kwastam, karin da aka yi, ya shafi harkokin cinikayya da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 84.5.

Wannan al'amari zai iya yin barazana ga farfadowar tattalin arzikin duniya da ci gabansa, da kuma batun samar da guraben ayyukan yi, in ji jami'in na WTO.

Ya yi gargadin cewa, matakai da ake bi na sanya shinge na keke-da-keke zai iya zama wata sabuwar al'ada a nan gaba, inda ya bukaci dukkan bangarori da su mayar da martani kuma su gaggauta lalibo hanyoyin warware matsalar.

Da yake jaddada irin muhimmayar rawar da WTO ke takawa wajen tabbatar da bunkasuwar duniya, ya ce kamata ya yi manyan shugabannin hukumomin ciniki na manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya su kara tattaunawa kan batun, kuma su samar da wani tsari na tuntubar juna karkashin manufofi da dokokin kungiyar ta WTO.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China