in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan mata miliyan 30 ne ke fuskantar hadarin kaciya a Afrika
2018-11-23 11:11:32 cri
Shugabar kwamitin kula da harkokin mata na majalisar dattawan Nijeriya, Binta Masi Garba, ta ce 'yan mata sama da miliyan 30 ne ke fuskantar hadarin kaciya a nahiyar Afrika.

Binta Masi Garba, wadda ta bayyana haka a jiya, a wajen taron mata na kasa da kasa a Afrika da aka yi a birnin Windhoek na Namibia, ta ce yaran nahiyar Afrika na ci gaba da fuskantar matsalolin da suka hada da talauci da rikici da kuma rashin damarmaki.

Ta ce daya daga cikin yara 6 da aka haifa a yankin kudu da hamada Sahara ba sa kai wa shekaru 5 saboda yunwa da cututtukan yara.

Ta kara da cewa, a watan Mayun 2014 nahiyar ta kaddamar da wani gangamin na kawo karshen auren wuri da kuma yunkurin dakile al'adu masu hatsari kamar kaciyar mata, amma har yanzu, a kasashen Afrika masu karanci da matsakaicin kudin shiga, a kan aurar da 1 cikin 'yan mata 3, yayin da suke da shekaru 8.

A don haka, Binta Masi Garba, ta yi kira ga gwamnatocin nahiyar Afrika su kara himmantuwa wajen kare 'yan mata ta hanyar zartar da dokar da za ta ba su kariya daga al'adu masu hadari a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China