in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin Afrika za su yi taro a Kenya game da muhalli
2018-09-16 16:26:57 cri
Ministocin muhalli na kasashen Afrika za su gudanar da taro a Nairobi wanda za a bude a gobe Litinin domin duba wasu dabaru da tsare tsaren da za a bullo da su wajen tunkarar matsalolin da suka shafi kare muhallai.

Hukumar kare muhalli ta MDD ta ce taron ministocin na Afrika karo na 7 za'a fara shi ne daga ranar 17 ga watan Satumba wanda ake sa ran ministiocin muhalli na kasashen Afrika 54 da kuma kwararru da wakilan kungiyoyin fararen hula daga kasashen Afrika za su halarci taron.

Sanarwar ta ce, ministocin za su yi nazari game da wasu tsare tsare wadanda za'a yi amfani da fasahohin zamani wajen aiwatar da su.

Ana sa ran sakamakon da aka samu a lokacin taron zai taimakawa kasashen Afrika wajen cimma matsaya da kuma samun muhimman bayanai game da yadda za'a tsara babban taron MDD game da muhalli wanda zai gudana a shekarar 2019.

Haka zalika sanarwar ta ce taron zai baiwa nahiyar dama game da shirya taro kan sha'anin muhalli karo na 14 karkashin yarjejeniyar MDD game da kare tsirrai da dabbobi dake neman bacewa daga doron kasa wanda zai gudana tsakanin ranar 17 zuwa 29 ga watan Nuwamba a kasar Masar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China