in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban darektan WTO:Lokaci ya yi na tattauna tsarin cinikayya
2018-07-25 09:55:41 cri

Babban darektan hukumar cinikayya ta duniya (WTO) Roberto Azevedo ya yi kira ga dukkan wadanda suka yi imani da harkar cinikayya a matsayin matakin ci gaba, da su fito karara don ganin an kare wannan tsari, ganin yadda tattalin arziki ke fuskantar barazana, biyo bayan karuwar zaman zullumi a harkokin cinikayyar duniya.

Azevedo ya yi wannan kira ne yayin rufe taron dukkan mambobin hukumar WTO. Yana mai cewa, mambobin hukumar sun san yadda zaman zullumi da rikicin cinikayya ke karuwa a duniya, baya ga sabbin matakai da ake kara dauka, kuma wannan abin damuwa.

Jami'in ya ce, duk yadda aka kalli lamarin, ko tantama babu an fara yakin cinikayya. Kuma karuwar hadarin hakan zai yi mummunan tasiri ga tattalin arziki, wadda daga bisa ni zai haifar da babbar bazarana ga kokarin samar da ayyukan yi, da ma yadda kasashen duniya ke kokarin farfadowa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China