in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Har abada ba za a manta da Kofi Annan ba
2018-08-20 19:14:03 cri

Yau Litinin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin Sin na mika sakon ta'aziya matuka game rasuwar tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sako ga babban sakataren MDD Antonio Guterres, domin nuna juyayi, inda ya bayyana cewa, Annan tsohon abokin al'ummun kasar Sin ne, ya kuma kware kan aikin siyasar kasa da kasa, kana fitaccen 'dan siyasa ne da ya fito daga kasar Afirka.

A hannu guda kuma, kokarin da ya yi ya kara karfafa aminci, da imanin al'ummun kasashen duniya kan makomar MDD, haka kuma ya kara jawo hankulan al'ummun kasashen duniya kan kasashen Afirka.

Ya ce mun hakake cewa, ba za a manta da shi ba har abada saboda babbar rawar da ya taka kan ci gaban bil Adama. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China