in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan inganta kiyaye zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya
2018-11-22 10:34:24 cri
Manzon musamman na kasar Sin dake kula da batun Gabas ta tsakiya, Gong Xiaosheng, wanda a halin yanzu ke ziyara a yankin Falesdinu, ya bayyana a jiya Laraba a birnin Ramallah cewa, kasar Sin na fatan kara taka muhimmiyar rawa kan batun Gabas ta tsakiya, da sa kaimin kiyaye zaman lafiya a shiyyar.

Gong ya gana da shugaban Falesdinu Mahmoud Abbas a ranar 20 ga wata, kana ya zanta da mamban kwamitin tsakiya na kungiyar Fatah, kuma kwamishinan kula da batun alaka da kasar Sin Abbas Zaki a ranar 21 ga wata.

A yayin taron manema labaru da aka shirya bayan ganawar, Gong ya ce, ana ta samun lamuran zubar jini a ko wace rana a yankin Gabas ta tsakiya, kuma kasar Sin tana bakin ciki, da kulawa sosai kan hakan. Kana tana son kara tallafawa yankin, da kuma kara taka muhimmiyar rawa kan batun.

Bayan haka kuma, Gong ya bayyana cewa, burin sa game da ziyarar da yake yi a yankunan Falesdinu da Isra'ila su ne, da farko domin nuna cewa, kasar Sin na dora muhimmanci kan batun Gabas ta tsakiya, bayan barkewar rikici a sabon zagaye a tsakanin Falestinu da Isra'ila, tare kuma da nuna goyon baya ga jama'ar yankin. Na biyu, domin inganta zaman lafiya, da nunawa shugabannin yankin matsayin da kasar Sin ke dauka, da kuma damuwarta kan ricikin.

Tun daga ranar 11 ga wata, aka samu barkewar riciki a sabon zagaye tsakanin Falestinu da Isra'ila. A karkashin shiga tsakani da kasashen duniya ke yi, ciki har da kasar Masar, an kwantar da ricikin a ranar 13 ga wata. Ricikin da ya haddasa rasuwar Falestinawa a kalla 14, tare da raunata wasu fiye da 10.

A ranar 20 ga watan nan ne dai manzon musamman na kasar Sin Gong Xiaosheng ya isa yankin Falesdinu, don gudanar da ziyara a yankunan Falestinu da Isra'ila. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China