in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da takwaransa na Palesdinu sun aika wa juna sakon murnar cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya
2018-11-20 19:42:31 cri

Yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Palesdinu Mahmoud Abbas sun aikawa juna sakon murnar cika shekaru 30 da kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu.

A ciki sakon, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, kasar Sin daya ce daga cikin kasashe wadanda suka goyi bayan nuna adalci ga Palestinawa, kuma daya daga cikin kasashe wadanda suka amince da kungiyar 'yantar da Palestinawa, kana daya daga cikin kasashe wadanda suka kulla huldar diplomasiya da kasar Palesdinu tun farkon kafuwarta. A cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata, kasashen biyu sun gudanar da hadin kai a fannoni da dama lami lafiya, haka kuma sassan biyu sun samu sakamako mai gamsarwa. Har kullum kasar Sin tana goyon bayan nuna adalci ga maido da halattun hakkokin al'ummarta, da goyon bayan kafa kasar Palesdinu mai cikakken yanci bisa tushen iyakar kasa da aka shata a shekarar 1967 da kasancewar gabashin birnin Kudus a matsayin hedkwatarta. Kasar Sin za ta ci gaba da kokarin ganin an gudanar da shawarwari a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, kuma za ta ci gaba da taka rawa domin warware batun Palesdinu bisa adalci daga duk fannoni.

A nasa bangare, shugaba Abbas ya bayyana a cikin sakonsa cewa, yana alfahari matuka da huldar aminci dake tsakanin kasashen biyu da ma al'ummominsu, kana ya yaba da kasar Sin saboda goyon bayan da take bayarwa kan muhimman batutuwa da suka shafi Palesdinawa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China