in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Amurka ya halarci liyafar shekara-shekara ta kwamitin NCUSCR
2018-11-18 15:58:36 cri
Jakadan kasar Sin a Amurka, Cui Tiankai ya halarci liyafar shekara-shekara ta kwamitin kula da dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin wato NCUSCR ta bana, a ranar Alhamis da ta gabata.

Da yake jawabi, Cui Tiankai ya bayyana cewa, a bana Sin ke cika shekaru 40 da aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida. Har ila yau, a bana ake cika shekaru 40 da gabatar da sanarwar kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka. Ya ce cikin shekarun 40 da suka gabata, an raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata bisa kokarin da bangarorin biyu suka yi, tare da samun gagarumar ci gaba a wannan fanni. Ya ce Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun ci gaba cikin lumana, wadda manufa ce da ba za ta sauya ba har abada.

Cui Tiankai ya kara da cewa, yayin da ake kokarin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, bangarorin biyu muhimman abokan hadin gwiwa ne, don haka ya kamata a daidaita dangantakar dake tsakaninsu ta yadda za ta dace da yanayin da ake ciki a karni na 21, da cimma burin kawar da rikici da kiyayya da juna, kana da girmama juna da hadin gwiwar samun moriyar juna don cimma burin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu mafiya karfi yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China