in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin ta musunta zargin Amurka na cewa wai Sin tana yin cinikayya dake gurgunta moriyar Latin Amurka
2018-10-30 19:06:47 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan kasar Amurka, za ta samar da taimakonta ga kasashen dake yankin Caribbean kamar yadda kasar Sin take yi. Lu Kang ya yi kiran ne a yau Talata, yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing. Ya ce a kwanan baya, yayin da ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yake ziyara a kasashen Panama da Mexico, ya zargi kasar Sin cewa, tana gudanar da cinikayyar dake gurgunta moriyar yankin Latin Amurka.

Game da hakan, firayin ministan kasar Antigua da Barbuda Gaston Browne, ya zanta da manema labarai, inda ya bayyana cewa, zargin ba shi da tushe ko kadan, kuma kamata ya yi Amurka ta ji kunya, bisa manufar da take aiwatarwa a yankin. Kana ya yi nuni da cewa, yankin Carribean zai rasa makoma mai haske idan har kasar Sin ta dakatar da samar masa taimako.

Mr. Lu Kang ya bayyana cewa, Amurka na sukar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa yadda take so, kuma ba wannan ne karo na farko ba, yana fatan Amurka za ta daina yin haka, kuma akwai bukatar Amurka ta rika samar da taimako ga kasashe masu tasowa, ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China