Rahotanni sun bayyana cewa, a kwanan baya, "mataimakin ministan tsaron hukumar yankin Taiwan" ya je jihar Maryland ta kasar Amurka, domin halartar taron masana'antun tsaron kasa, tsakanin Amurka da Taiwan, taron da mai taimakawa ministan tsaron kasar Amurka ya halarta, ya kuma gabatar da jawabi.
Kan wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta bukaci gwamnatin Amurka, da ta martaba ka'idar nan ta kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da ka'idojin da aka tanada, a cikin hadaddun yarjejeniyoyi uku da kasashen biyu suka daddale. Haka kuma, ta daina yin cudanya tsakaninta da Taiwan bisa matsayin gwamnatoci ko kuma kan aikin soja.
Lu Kang ya ce kasar Sin ta kuma bukaci Amurka, da ta daina sayar da makamai ga Taiwan, ta daidaita hulda kai tsaye tsakaninta da Taiwan, in ba haka ba, akwai yiwuwar lamarin ya gurgunta huldar dake tsakanin Sin da Amurka, tare kuma da lalata zaman karko a zirin Taiwan.(Jamila)