Yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin na mai da hankali matuka kan hakkin dan Adam, haka kuma tana kokarin kyautata yanayin da al'ummun kasar ke ciki a fannin, a don haka ta bukaci Amurka da ta kara dora muhimmanci kan yanayin kiyaye hakkin dan Adam da take ciki, kuma kada ta ci gaba da tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashe, ta hanyar fakewa da siyasar kiyaye hakkin dan Adam.(Jamila)