NLC dai ta yi barazanar ci gaba da gudanar da yajin aikin ne na sai baba ta gani, tun daga Larabar nan har zuwa lokacin da gwamnatin za ta janye karin da aka samu a wadannan fannoni biyu.
Jagororin kungiyar da magoya bayan su sun yi fitar dango da safiyar yau Laraba, daga hedkwatar kungiyar dake tsakiyar birnin Abuja, sa'an nan suka yi tattaki kan titunan birnin, bayan sauraron jawabin jagoran kungiyar Aliyu Wabba. Masu zanga-zangar dake rike da alluna da kwalaye dake dauke da sakwannin nuna fushin su ga matakin gwamnatin tarayyar, sun ce za su ci gaba da gudanar da jerin gwanon a kullum, har sai lokacin da gwamnatin ta sauya matsaya.
Yayin zaman tattaunawa da sassan biyu suka kammala a daren ranar Talata, an tashi ba tare da cimma cikakkiyar matsaya ba, sai dai tsagin gwamnatin Najeriyar ya ce zai iya duba yiwuwar kara albashin ma'aikata, tare da daukar wasu matakai na rage radadin da karin farashin na mai ka iya haifarwa.(Saminu)