in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaman jami'o'i sun shiga yajin aiki a Najeriya
2016-11-17 09:34:11 cri

Malaman jami'o'in gwamnati a Najeriya sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki 7 a duk fadin kasar tun daga jiya Laraba, sakamakon zargin da suke yiwa gwamnatin kasar na rashin cika alkawurran da da ta daukar musu.

Kungiyar ta malamam jami'o'i wato ASUU, ta bayyana cewa, dole ne ta shiga yajin aikin domin tunatar da gwamnatin kasar game da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kungiyar da mahukuntan kasar tun a shekarar 2009.

Mafi yawa daga cikin yarjejeniyoyin sun shafi inganta albashin malaman jami'o'in kasar ne.

Biodun Ogunyemi, shi ne shugaban kungiyar ASUU na kasa, ya bayyana cewa, matsalar rashin ware isassun kudade a fannin ilmi cikin kasafin kudin kasar yana daga cikin dalilan gudanar da yajin aikin.

Majalisar dattijan Najeriya ta nemi shiga tsakani a lokacin zaman majalisar na ranar Talatar da ta gabata, to sai dai yunkurin majalisar bai yi nasara ba.

A wani labarin kuma, gwamnatin Najeriyar ta bayyana yajin aikin a matsayin yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China