in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lauyoyi da alkalan kotuna a Sudan ta Kudu sun shiga yajin aiki na kasa baki daya
2017-05-03 09:48:56 cri

A jiya Talata ne majalisar lauyoyi da alkalan kotuna ta kasar Sudan ta Kudu ta ayyana shiga yajin aiki na kasa baki daya saboda batutuwan da suka shafi harkokin mulki da yanayin aiki.

Shugaban kwamitin lauyoyi da alkalan kasar, Khalid Abdalla Mohammed ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, dukkan kotuna da ke kasar za su dakatar da ayyukansu, bayan tattaunawar da ofishin shugaban kasar ya jagoranta da nufin kawo karshen takaddamar dake tsakanin alkalai da babban mai shari'a na kasar ya ci tura.

Wannan yajin aikin na zuwa ne bayan da uwar kungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta shiga a makon da ya gabata, domin fara sasantawa da shugaba Salva Kiir na kasar. Kungiyar dai tana bukatar ko dai a cire babban mai shari'a na kasar Chan Reec Madut ne, ko kuma ya yi murabus daga mukaminsa.

Har ila alkalan suna bukatar a kafa wasu dokokin da suka shafi ma'aikatan shari'a, da samar musu da alawus na sufuri, da inganta yanayin aikinsu, kana a samarwa ko wane alkali dake fadin kasar dakin hutawa a kotunan da suke aiki da sauransu.

A shekarar da ta gabata ce dai alkalai a fadin kasar Sudan ta Kudun suka shiga wani dogon yajin aiki na wata guda, inda suka gabatar da makamantan wadannan korafe-korafe da suka gabatar a wannan shekara.

Sai dai daga bisani sun dakatar da yajin aikin, bayan da gwamnati ta amince ta biya musu bukatun nasu, amma har yanzu ba ta cika wasu daga alkawuran da alkalan suka gabatar mata ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China