in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sanya hannu kan takardar hadin kai tare da ASEAN
2018-11-14 20:15:40 cri
Yau aka bude taron shugabanni tsakanin Sin da kasashe mambobin ASEAN karo na 21 a kasar Singapore, inda firaministan kasar Sin Li Keqiang, da shugabanni na kasashe mambobin ASEAN, suka tattauna tare kuma da zartas da wata takarda, game da burin da ake fatan cimmawa, kan inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da mambobin kungiyar ASEAN nan da shekarar 2030.

Da wannan mataki, kasar Sin ta kasance abokiyar kawance ta farko, wadda ta tsara shiri mai matsakaici da dogon zango, game da makomar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu wato Sin din da kuma kungiyar ASEAN. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China