in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron musamman a tsakanin ministocin harkokin waje na kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN
2016-06-15 10:14:45 cri

An yi taron musamman a tsakanin ministocin harkokin waje na kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN a jiya Talata a birnin Yuxi na lardin Yunnan, inda kuma ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi da ministan harkokin waje na kasar Singapore, wadda ke gudanar da aikin shiga tsakani a cikin kungiyar ASEAN suka shugabanci taron.

Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar ASEAN sun yaba wa ci gaban dangantaka da musayar ra'ayi dake tsakanin kungiyar da kasar Sin sosai, kana bangarorin biyu sun nanata niyyarsu ta kiyaye zaman lafiya a yankin tekun kudancin kasar Sin.

A gun taron manema labaru da aka kira bayan taron, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, ministocin harkokin waje na kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN sun tattauna sosai kan batun tekun kudancin Sin domin kara fahimtar juna, inda suka jaddada cewa, za su kiyaye zaman lafiya a wannan yanki tare domin tabbatar da tsaro da wadata a yankin. Bugu da kari, sun nanata cewa, ya kamata a daidaita batun tekun kudancin Sin yadda ya kamata, domin kaucewa mummunar illa da batun zai haifar wa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kungiyar ASEAN.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China