in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomi a Morocco sun dakile yunkuri 68,000 na shigar bakin haure kasar cikin watanni 9
2018-11-09 16:06:33 cri

Ministan kula da harkokin cikin gidan Morocco, Abdelouafi Laftit, ya ce hukumomi a kasar, sun ce sun dakile yunkuri 68,000 na shiga kasar ba bisa ka'ida ba, tsakanin watan Junairu zuwa Satumba.

Kamfanin dillancin labarai na MAP, ya ruwaito ministan na cewa, cikin watanni 9 a farko na 2018, sun datse hanyoyin safara 122.

Abdelouafi Laftit, ya kara da cewa, hukumomin tsaro sun kara kaimi ga yaki da hanyoyin safara da fasa kauri, wadanda ake amfani da su wajen jigilar bakin haure.

Ya ce, wasu bakin haure 50,000 da za su bar kasar sun amfana daga matakai 2 na aikin amincewa da su, adadin shi ne kaso 85 na jimilar mutanen da suka nemi izinin amincewa daga gwamnatin kasar da baki daga kasashe 113 suka gabatar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China