in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama dan Najeriya da laifin safarar cocaine a Morocco
2018-08-13 10:26:12 cri

An damke wani dan Najeriya a filin jirgin saman kasa da kasa na Mohammed V dake Casablanca na kasar Morocco bisa zarginsa da safarar hodar iblis, 'yan sandan Moroccan sun sanar da hakan a jiya Lahadi.

A cewar sanarwar 'yan sandan, an samu hodar iblis din mai nauyin kilogram 1.85 a cikinsa a asibitin Casablanca.

Wanda ake zargin yana shirin tafiya ne zuwa birnin Sao Paulo, na kasar Brazil, in ji majiyar.

A halin yanzu ana tsare da mutumin har zuwa lokacin kammala bincike.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China