in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco za ta karbi bakuncin taron gamayyar kasa da kasa kan yaki da IS
2018-06-25 10:39:50 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Morocco ta sanar da cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gamayyar kasa da kasa don yaki da kungiya mai da'awar kafa daular Islama (IS) a ranar Talata a babban birnin kasar Rabat, domin tattaunawa game da barazanar da kungiyar IS ke yiwa nahiyar Afrika.

Taron, wanda shi ne irinsa na farko wajen hada karfi da karfe, zai samu halartar mambobin kasashen gamayyar, da kasashen Afrika da shiyyoyi da kuma kungiyoyin kasa da kasa.

Sanarwar ta ce, makasudin shirya taron shi ne domin bibiyar irin ci gaban da aka samu wajen dakile barazanar kungiyar ta IS a Afrika da kuma tattaunawa game da burin da kungiyar ke son cimmawa a kasashen na Afrika.

Haka zalika, taron zai kuma binciko hanyoyin da za'a bi wajen yin hadin gwiwa da hada kai da bangarorin da abin ya shafa don magance barazanar kungiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China