in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta yi kira da a kawo karshen tushen ta'addanci a Afrika
2018-06-27 10:04:15 cri

Ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita, ya yi kira da a magance musababbin tushen ta'addanci a Afrika.

Nasser Bourita, wanda ya bayyana haka jiya a birnin Skhirate na kasar, yayin bude taron kawance kasashen duniya kan yaki da kungiyar IS, ya jadadda cewa, ingancin yaki da ta'addanci a Afrika na bukatar duba musababbin matsalar daga tushe, yana mai cewa, idan ba haka ba, hakarsu ba za ta cimma ruwa.

Ministan ya kuma yi gargadi game da komawar mayakan IS Afrika daga yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai jadadda bukatar hadin kan kasashen Afrikan.

Nasser Bourita, ya kuma bayyana cewa, kasarsa ta kuduri niyyar zama misali na hadin kai da sauran kasashen Afrika, ta yadda za a samu ingantacciyar hadin gwiwa da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a nahiyar, tare da sanya al'ummar nahiyar kan gaba a cikin ayyukan gwamnatoci na bai daya.

Taron wanda shi ne irinsa na farko, ya hada kasashen Afrika da kuma wasu hukumomin yankuna da na duniya.

Manufar taron ita ce, nazarin barazanar kungiyar IS a Afrika da lalubo hanyoyin hadin gwiwa da karfafa hadin kai tsakanin masu ruwa da tsaki domin tunkarar barazanar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China