in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan tana maraba da shirin Amurka na tsame ta daga jerin kasashe 'yan ta'adda
2018-11-09 10:22:43 cri

Gwamnatin kasar Sudan ta ce, tana maraba da shirin da kasar Amurka ke yi na tsame Khartoum daga cikin sunayen kasashen duniya dake daukar nauyin ayyukan ta'addanci.

"Sudan tana maraba da sanarwar da Amurka ta fitar game da shirin da take yi na tsame kasar Sudan daga cikin kasashen duniya masu daukar nauyin ayyukan ta'addanaci da kuma kokarin karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu." in ji wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Sanarwar ta nanata aniyar kasar ta Sudan na amincewa da shiga tattaunawa a zagaye na biyu tsakanin Washington da Khartoum domin cimma bukatar da aka sanya a gaba.

Sanarwar ta kara da cewa, Sudan ta amince ta shiga zagaye na biyu na muhimmiyar tattaunawar wadda aka tsara da nufin karfafa mu'amalar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma samun karin ci gaba a dukkannin fannoni da suka shafi kasashen biyu, musamman bayan nasarar da aka cimma a zagayen farko wanda shi ne ya yi sanadiyyar Amurkar ta dagewa Sudan takunkumin tattalin arzikin da ta aza mata a shekarun baya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China