in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in diplomasiyyar Amurka ya ce dage takunkumi kan Sudan zai fara aiki nan take
2017-01-17 10:31:19 cri

A jiya Litinin wani jami'in diplomasiyyar Amurka ya ce, matakin gwamnatin kasarsa na dage takunkumi kan kasar Sudan, zai fara aiki ne tun daga yau Talata.

Jami'in na Amurka Steven Koutsis, ya shedawa 'yan jaridu a Khartoum cewa, matakin da shugaban kasar Barack Obama ya dauka na dage takunkumin cinikayya kan Sudan zai fara aiki ne nan take tun daga yau Talata.

Ya bayyana cewa, gwamnatin Sudan ta kasance tana hadin gwiwa da Amurka wajen yaki da ta'addanci.

Ya ce, wannan mataki da Amurkar ta dauka, zai baiwa kasar ta Sudan damar yin amfani da kudadenta da ta adana a bankunan kasar Amurka, domin kammala wasu muhimman ayyuka, da kuma zuba jari a fannin man fetur da albarkatun kasa, kana wannan mataki zai kara karfafa hadin kan dake tsakanin kasashen na Sudan da Amurka.

A ranar 13 ga watan Janairu ne, Obama ya soke matakin da Amurkar ta dauka na kakabawa Sudan takunkumin tattalin arziki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China