Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya ce ya kamata a kaucewa mummunan tasirin takunkumai a kan Libya, sannan bai kamata su shafi rayuwar fararen hula ba.
Ma Zhaoxu, ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD a jiya cewa, takunkuman ba manufofi ba ne, don haka bai kamata su shiga rayuwar fararen hulan kasar ba.
Kasar Sin ta kuma bukaci kasa da kasa su kara mara baya ga farfadowar doka da oda a Libya, domin samar da maslahar siyasa da za ta kunshi kowa da kowa. (Fa'iza Mustapha)