in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin a MDD ya ja hankalin kasashen duniya game da yaki da ta'addanci
2018-08-25 15:27:53 cri

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada karfi waje guda, domin yaki da ayyukan ta'addanci.

Wu haitao wanda ya bayyana hakan ga mambobin kwamitin tsaron MDD ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su bi tsari guda, tare da nuna matukar kyama ga ayyukan 'yan ta'adda. Ya ce yayin da ake yaki da ayyukan ta'addanci a mataki na kasa da kasa, ya zama wajibi a kiyaye 'yancin kan kasashe masu ruwa da tsaki, a kuma yi biyayya ga dokokin MDD, tare da tallafawa MDDr, da kwamitin tsaron ta, wajen taka rawar da ta dace.

Kaza lika wakilin na Sin, ya bayyana bukatar hada kai da karfi, wajen magance dalilan dake haifar da ayyukan ta'addanci tun daga tushen su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China