in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Sin ya bayyana samar da ci gaba a matsayin tushen zaman lafiya
2018-07-04 10:22:47 cri

Wani jami'in diplomasiyyar kasar Sin ya ce, hanya daya tilo da kasashen duniya za su yi amfani da ita wajen magance tashe tashen hankula ita ce samar da ci gaban al'ummarsu, da kare 'yancin dan adam, da kuma samarwa al'ummarsu ingantacciyar rayuwa.

Yu Jianhua, shugaban tawagar wakilan kasar Sin a MDD a birnin Geneva, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin taron kwamitin kare hakkin dan adam na MDDr karo na 38, a cikin wani jawabinsa mai taken "Gudumowar ci gaba da rage talauci wajen bunkasa da kuma kare hakkin dan adam".

Yu ya jaddada cewa, game da samun kyakkyawar makoma da fuskantar kalubaloli, wajibi ne kasashen duniya su yi amfani da raya ci gaba a matsayin jigo.

Yu ya fadawa mahalarta taron cewa, "Ci gaban da muke fata dole ne ya kasance an samar da damammaki na daidai wa daida, dole ne a shigar da kowane bangare domin amfanar da dukkan bangarori; dole ne ya kasance cikakken tsari wanda zai kasance a matsayin tushe, dole ne ya kasance mai cike da fasaha wanda zai samar da makomar bunkasa ci gaba".

Yu ya ce, kasar Sin tana mai da hankali kan rayuwar al'umma a kokarin da take wajen kirkire-kirkire, da zaman jituwa, da kiyaye muhalli, da bude kofa, da kuma moriyar juna, kuma ta samu babban sakamako mai gamsarwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China