in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu nasarori wajen aiwatar da manufofin da suka shafi kananan kabilu
2018-08-14 09:44:05 cri

Ana ci gaba da nazarin yadda ake aiwatar da manufofin da kasar Sin ke son cimmawa dangane da kare hakkin bil adama tsakanin 2016-2020, kuma zuwa yanzu, an samu nasarori wajen cimma manufofin da suka shafi kananan kabilu.

Darakta janar na sashen kulla yarjejeniya da kare dokokin kasar Sin a ma'aikatar harkokin wajen kasar Xu Hong ne ya bayyana haka, a lokacin da yake ganawa da mambobin kwamitin MDD dake yaki da wariyar launin fata, wanda ke nazarin rahoton kasar Sin game da aiwatar da muradunsa.

Xu Hong, ya shaidawa mambobin kwamitin cewa, ana tabbatar da hakkokin kananan kabilu ta fuskar jin ra'ayoyinsu da kuma damawa da su cikin harkokin gudanarwar kasar.

Ya ce, a yanzu, dukkan kananan kabilun kasar Sin 55 na da wakilci a majalisar wakilan kasar da kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar.

Ya kara da cewa, jami'ai daga kananan kabilu ne ke shugabantar harkokin gudanarwa a yankuna 155 masu cin gashin kansu na kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China