in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da mutuwar mutane 3 sanadiyyar kifewar kwale-kwale a Nijeriya
2018-11-09 10:08:12 cri

Gwamnatin jihar Lagos dake kudancin Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar mutane 3, yayin da wasu 5 suka bata, sanadiyyar kifewar kwale-kwale a jihar.

Fasinjoji 20 ne ke cikin kwale-kwalen a lokacin da ya kife da yammacin ranar Laraba, a kusa da tsibirin Tin Can.

Kwale-kwalen ya kife ne mintoci kalilan bayan tashinsa, inda ya nufi garin Ojo dake wajen birnin Lagos.

Babban manajan hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, Adesina Tiamiyu, ya shaidawa manema labarai cewa, an ceto mutane 12, kana ana ci gaba da aikin neman wadanda suka bace.

Ya kara da cewa, tuni aka kaddamar da bincike don gano musababbin hatsarin. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China