in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Najeriya sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa kan aikin samar da wutar lantarki
2018-11-06 18:55:56 cri

Yau Talata rukunin masana'antun babbar ganuwa wato CGWIC na kasar Sin wanda ke jagorar kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar ya daddale yarjejeniyar hadin gwiwa kan aikin samar da wutar lantarki da hukumar kula da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a na kimiyya da gine-gine ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta tarayyar Najeriya a birnin Zhuhai na lardin Guangdong dake kudancin kasar ta Sin, lamarin da ya alamanta cewa, hadin gwiwar dake tsakanin rukunin CGWIC da Najeriya ya habaka daga fannin harkokin sararin samaniya zuwa sauran fannoni.

Bisa kwangilar da sassan biyu suka daddale, rukunin CGWIC zai kammala aikin kera na'urorin samar da wutar lartarki da na'urorin sanin iya wutan da aka yi amfani da shi, da dakin daidaita karfin wuta, da na'urorin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da hasken rana nan da watanni 30 daga lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki, kwatankwacin adadin kudin kwangilar ya kai dalar Amurka miliyan 300. Idan kamfanin kasar Sin ya kammala wannan babban aiki, to zai taka rawa wajen samar da wutar lantarki a kasar Najeniya, har ma zai taimaka ga ci gaban tattalin arzikin kasar, kana Najeriya za ta iya fitar da lantarki zuwa ga sauran kasashe makwabtaka, domin samun riba mai tsoka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China