in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Za a dauki matakan musamman game da ruwa da tsaftar muhalli
2018-11-09 10:00:24 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ayyana shirin gwamnatin sa na daukar kwararan matakai, domin tabbatar da tsaftar muhalli, da samar da ruwa mai tsafta ga daukacin al'ummar kasar.

A jiya Alhamis ne shugaba Buhari, ya umarci daukacin hukumomin gwamnatin kasar a dukkanin matakai da su kara azama, wajen aiwatar da manufofin samar da tsaftatacciyen ruwan sha, da inganta tsaftar muhalli, matakin da a cewar sa, gwamnati za ta sanya gaba har sai an kai ga cimma nasara.

Shugaba Buhari ya ce, ayyana wannan mataki ya zama dole, duba da bukatar da ake da ita, ta dakile yaduwar cutattukan da ake dauka ta ruwa dake haddasa yawan mace macen al'umma a dukkanin sassan kasar.

Shugaban na Najeriya ya kuma kaddamar da shirin tsaftar ruwa, da muhalli, da kiwon lafiya, wanda aka yiwa lakabi da "WASH", shirin da zai taimaka wajen cimma burin kawo karshen yin ba haya a waje nan da shekarar 2025.

Yayin kaddamar da shirin na "WASH", shugaba Buhari ya bayyana damuwa, game da yawan alkaluman al'ummun kasar da suke ba haya a waje sakamakon rashin ban dakuna, da karancin tsaftataccen ruwan sha, da tsaftar muhalli a daukacin kasar.

Wasu alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 1990, kason al'ummar kasar dake samun ruwan fanfo mai tsafta bai wuce 32 bisa dari ba, kana alkaluman sun ragu zuwa kaso 7 bisa dari a shekarar 2015. A daya bangaren kuma, kyautatuwar yanayin tsafta ya yi kasa daga kaso 38 bisa dari a shekarar 1990, zuwa kaso 29 bisa dari a shekarar 2015.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China