in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun hallaka mutane akalla 15 a arewacin Najeriya
2018-11-01 20:36:03 cri

Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, na cewa wasu da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne, sun hallaka akalla mutane 15, suka kuma cinnawa wasu gidaje wuta a kauyukan Kofa, da Abba Malumti dake Konduga.

Wani ganau ya shaidawa majiyar mu cewa, mutane da dama sun bace, tun bayan hare haren bindiga na daren jiya Laraba.

Wani mazaunin yankin Yahaya Danjuma, ya tabbatar da cewa, cikin wadanda 'yan bindigar suka hallaka, hadda limamin kauyen Kofa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China