in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa da nahiyar Afrika
2018-11-07 11:07:29 cri
Shugaban kwamitin tuntuba kan harkokin siyasa na al'ummar kasar Sin Wang Yang, ya ce kasar Sin za ta hada hannu da Afrika wajen inganta hadin gwiwa domin moriyar al'ummomin bangarorin biyu.

Wang Yang, ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da ayarin wakilan majalisun kula da tattalin arziki da zamantakewa na Tarayyar Afrika.

Ya kara da cewa nasarar taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika a watan Satumba, ya bude wani sabon babi ga dangantakar Sin da Afrika.

Har ila yau, ya ce kwamitin tuntuba kan harkokin siyasa na al'ummar kasar Sin, zai ci gaba da mara baya ga hadin gwiwa tsakanin majalisar kula da tattalin arzki da zamantakewa ta kasar Sin da cibiyoyi irinta na Afrika, domin zurfafa ci gaba ga muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu.

A nasa bangaren, Shugaban ayarin na Afrika Boulkassoum Haidara, ya ce a shirye Afrika take ta ba majalisaun kula da tattallin arziki da zaman takewa damar taka gagagrumar rawa wajen inganta hadin gwiwar moriyar juna a fannoni daban daban tsakanin bangarorin biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China