in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in Sin yana ziyarar kara bunkasa alaka a Jamhuriyar Congo
2018-06-14 09:17:15 cri

Shugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin Wang Yang ya kai wata ziyarar aiki Jamhuriyar Congo domin kara karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Yayin ganawarsa da shugaba Denis Sassou Nguesso na Jamhuriyar Congo a ranar Laraba da safe, Wang ya isar wa shugaba Nguesso sakon gaisuwa da fatan alheri daga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping.

Wang ya ce, ziyararsa a Jamhuriyar Congo, zango na farko a rangadin da ya fara kaiwa kasashen waje tun lokacin da ya kama aiki a watan Maris din wannan shekara, ya nuna irin yadda kasar Sin ke dora muhimmanci kan alakarta da kasar, da ma nahiyar Afirka.

Jami'in na kasar dai ya gudanar da ziyarar ce daga ranar Litinin zuwa Laraba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China