in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yang ya kai ziyarar aiki Uganda
2018-06-17 15:48:14 cri

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Wang Yang, ya gudanar da ziyarar aiki ta sada zumunta a kasar Uganda, tsakanin ranakun 13 zuwa 16 ga watan nan, bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi masa, inda ya gana da shugaban kasar Yoweri Museveni, da shugabar majalisar wakilan kasar Rebecca Alitwala Kadaga, da mataimakin shugaban kasar Edward Ssekandi, kana ya yi shawarwari da firayin ministan kasar Ruhakana Rugunda.

Yayin ganawarsa da shugaba Museveni, babban jami'in kasar ta Sin Wang Yang, ya mika masa gaisuwa da fatan alheri na shugaba Xi Jinping, kana Wang Yang ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, al'ummun kasar Sin suna kokari matuka, karkashin jagorancin tunanin shugaba Xi Jinping, game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, domin cimma burin "kafa zaman al'umma mai matsakaiciyar wadata a dukkan fannoni, a yayin da JKS ta cika shekaru 100 da kafuwa, da kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu na zamani mai wadata, da bin tsarin demokuradiya, da samar da wayewar kai, da kuma jituwa nan da shekara 2049, wato yayin bikin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama'ar Sin".

Ya ce kamata ya yi kasashen biyu wato Sin da Uganda, su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, bisa tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da kuma shawarar ziri daya da hanya daya. Ban da haka, har kullum kasar Sin tana goyon bayan daukacin kasashen Afirka, ciki har da Uganda wajen samun ci gaba yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaban Uganda Museveni ya bayyana cewa, shirin hadin gwiwa da ke kumshe da fannoni goma, wanda shugaba Xi ya gabatar, ya samar da sabuwar dama ga kasarsa ta Uganda, domin ta samu ci gaba cikin matsakaicin lokaci, da kuma dogon lokaci. Ya ce ya gamsu sosai da hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Uganda, haka kuma yana sa ran zai fidda tsarin raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka, a yayin taron kolin da za a kaddamar a birnin Beijing tare da shugaba Xi.

Yayin shawarwarinsa da firayinminista Rugunda kuwa, Wang ya bayyana cewa, yanzu haka ana gudanar da cudanyar manyan jami'an sassan biyu yadda ya kamata, haka kuma sassan biyu suna nuna wa juna goyon baya da fahimtar juna, a kan manyan batutuwan kasashen duniya, kuma kasar Sin tana sa ran Uganda za ta kara taka rawar gani a harkokin shiyya shiyya.

Shi ma Rugunda ya amince da cewa, ana tafiyar da huldar sassan biyu lami lafiya, kuma kasarsa ita ma ta samu babbar moriya daga hakan. Kana nan gaba za ta koyi fasahohin da kasar Sin ta samu na raya kasa. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China