in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yang ya ziyarci Kenya
2018-06-20 13:12:21 cri

Shugaban kwamitin majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin Wang Yang, ya kai ziyarar aiki a kasar Kenya daga ranar 16 zuwa 19 ga watan Yuni, inda ya gana da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, da shugaban majalisar dattawan kasar Kenneth Lusaka tare kuma da yin shawarwari da shugaban majalisar dokokin Kenya Justin Muturi.

Yayin ganawar tasa da Kenyatta, Mista Wang yana fata shugaba Kenyatta zai halarci taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika da za a gudanar a birnin Beijing a watan Satumba mai zuwa, don kara dankon zumuncin kasashen biyu, dandalin dai zai sanar da sabbin tsare-tsare na hadin gwiwar Sin da Afrika a sabon zamani a waccan lokaci.

A nasa bangaren, Kenyatta ya ce, Kenya ta nacewa goyon bayan kasar Sin ta fuskar daukar bakuncin taron kolin dandalin, kuma yana fatan kara tuntubar juna tsakanin shugabannin kasashen biyu nan gaba, da kara hadin gwiwa a fannin tsare-tsaren bunkasa kasashen biyu.

Yayin da Mista Wang ya yi shawarwari da Muturi, ya yi bayani kan yadda jam'iyyun daban-daban na Sin suke hadin gwiwa tsakaninsu da tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa, yana fatan kwamitinsa da majalisar dokokin Kenya sun bada gudunmawarsu don ciyar da hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da mu'ammalar al'adunsu gaba. Muturi ya ce, ko wace kasa na da 'yancin zabar tsarin siyasar da hanyar samun bunkasuwar da za ta bi, kasashen Kenya da Sin na mutunta hanyar da suka zaba, suna maida juna a matsayin aminai. Majalisarsa tana fatan kara yin mu'ammala da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kwamitin dake karkashin jagorancin Mista Wang, matakin da zai kawo yakini ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu nan gaba. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China