in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bikin CIIE Ya Bayyana Niyyar Kasar Sin Ta Bude Kofarta Ga Kasashen Ketare
2018-11-06 16:25:12 cri

A jawabin da ya gabatar a yayin taron dandalin Hongqiao na tattaunawar harkokin kudi da tattalin arziki tsakanin 'yan jarida da masana masu ba da shawara da aka gudanar a jiya Litinin da yamma, shugaban babban gidan rediyon da telebijin na kasar Sin CMG Mr. Shen Haixiong ya bayyana cewa, bayanai masu gamsarwa da ke cikin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin bikin kaddamar da baje kolin kayayyakin da ake shigo da su nan kasar Sin, sun jawo hankalin al'umma sosai, tare da samun amsa daga gida da kuma waje.

Shen Haixiong ya ce, a jawabin da ya gabatar, shugaba Xi Jinping ya bayyana matakan da kasar Sin ta dauka na kara bude kofarta ga kasashen waje, da kuma niyyarta ta cin moriyar juna tare da kasashen duniya. Har wa yau, yadda shugaba Xi ya kwatanta tattalin arzikin kasar Sin da teku da ma sauran bayanai masu gamsarwa dake cikin jawabinsa sun burge jama'a sosai tare da samun tsokaci daga gare su.

A matsayinsa na wani babban bikin baje kolin na kasa da kasa na farko da ke dora muhimmanci kan shigo da kaya a duniya, bikin nan na CIIE ya nuna niyyar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen ketare, da ra'ayinta na sa himma wajen bude kasuwa ga duniya, kana ya nuna wa kasashe daban daban cewa, Sin na maraba da su wajen shiga da kuma more sabuwar dama da take samarwa sakamakon ci gaba.

Shen Haixiong ya ce, a kwanakin baya, shugaba Xi Jinping ya ba da wani muhimmin jawabi a lardin Guangdong, wato wurin da aka soma gudanar da manufar yin kwaskwarima cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, inda ya kara bayyana niyyar kasar Sin ga duk duniya yana mai cewa, kasar ba za ta dakatar da bin manufar ba, kuma tana fatan more dama mai kyau da take samarwa wajen samun ci gaba. A ganinsa, idan jawabin nan da shugaba Xi Jinping ya yi a Guangdong ya sanar da cewa, kasar Sin za ta zurfafa yin kwaskwarima, to jawabin da ya yi a bikin bude baje kolin CIIE ya nuna cewa, kasar Sin za ta zurfafa bude kofa ga kasashen ketare.

Baya ga haka, Shen Haixiong ya nuna cewa, rahoton da bankin duniya ya bayar a kwanaki 5 da suka wuce game da muhallin cinikayya a shekarar 2019 ya nuna cewa, matsayin kasar Sin game da muhallin cinikayya ya karu da 32 idan aka kwatanta da bara. Hakan ya nuna cewa, muhallin tattalin arzikin kasuwanni na kasar Sin yana ta kara samun karbuwa a wajen kasashen duniya. (Masu fassarawa Lubabatu Lei, Bilkisu Xin, Ma'aikatan sashen Hausa)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China