in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan jaridar kasar Sudan na fatan bikin CIIE zai taimaka ga kyautata tattalin arzikin duniya
2018-11-06 13:01:08 cri
Darektan sashen kula da labaran tattalin arziki na jaridar Sudan Vision Daily Mohammed Abdalla, wanda yanzu haka yake halartar taron dandalin Hongqiao na tattaunawar harkokin hada-hadar kudi da tattalin arziki tsakanin 'yan jarida da kwararru, ya bayyana jiya Litinin a birnin Shanghai cewa, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin, kasaitaccen biki ne ta fannin tattalin arziki da cinikayya, wanda ba a taba ganin irinsa ba, kuma yana fatan bikin zai taka muhimmiyar rawa a fannin inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya da kuma ciniki maras shinge.

Ya kara da cewa, "A jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya yi kira ga kasa da kasa da su hada karfinsu, don samar da 'yancin yin ciniki, tare da nuna rashin amincewa da manufar kariyar ciniki da kuma tsarin yin gaban kai. Ya ce a ganinsa, dunkulewar kasashen duniya baki daya abu ne da zai amfana wa kasa da kasa, sai dai akwai 'yan tsirarrun kasashen da suke kyamarta tare da neman janye jikinsu."

Mohammed Abdalla ya kuma ce, bikin baje kolin da ake gudanarwa yanzu da ma sauran matakan da kasar Sin ta dauka na bude kofarta, sun bayyana niyyar kasar ta inganta harkokin ciniki cikin yanci a duniya da ma samar da sauki ga harkokin da suka shafesu, Ya na mai fatan tattalin arzikin kasar Sudan ma zai amfana.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China