in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya sanar da sabbin matakan kasar Sin na bude kofa ga waje a yayin bikin CIIE
2018-11-05 15:05:06 cri
Yau Litinin, aka bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa dasu kasar Sin karo na farko wato CIIE a birnin Shanghai na kasar, shugaban kasar Xi Jinping ya halarci bude bikin, inda kuma ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Bikin CIIE bikin baje koli ne irin sa na farko a duniya, wanda aka mayar da batun shigowa da kayayyaki a matsayin babban takensa bisa shawarar da Shugaba Xi ya bayar. Bikin CIIE na wannan karo ya samu halartar kasashe da yankuna da ma kungiyoyin duniya 172, tare kuma da kamfanoni fiye da 3600. Haka kuma an kiyasta, 'yan kasuwa na gida da na waje kimanin dubu 400 ne zasu shiga biki don cinikayya.

A cikin jawabin da ya gabatar, Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, shirya bikin CIIE wata babbar manufa ce da kasar Sin ta fitar, wajen bude kofa ga waje, kuma wani muhimmin mataki ne da Sin ke dauka, wajen bude kasuwarta ga duniya. Lamarin da ya shaida matsayin kasar Sin, na goyon bayan tsarin yin cinikayyar kasa da kasa, da sa kaimi ga yin ciniki maras shinge.

Xi ya ce, yanzu ana kokarin kyautata tattalin arzikin duniya, a sa'i guda ana samun farfadowar ra'ayin bada kariya da ra'ayin bangare guda, tare kuma da fuskantar kalubale wajen neman dunkulewar tattalin arzikin duniya, banda haka kuma, ana gamuwa da matsaloli a fannonin ra'ayin bangarori da dama, da tsarin cinikayya cikin 'yanci, har zuwa yanzu ana fuskantar rashin tabbaci. Don haka, kamata ya yi a kara fahimtar yanayin da ake ciki, da tsayawa kan aniyar bude kofa da hadin kai, don tinkarar hadari da kalubaloli tare.

Sa'an nan, shugaba Xi ya yi kira ga kasashe daban daban dasu tsaya kan matsayinsu na bude kofa, da yin mu'amala da juna domin fadada damammakin yin hadin gwiwar moriyar juna. Sannan su tsaya kan matsayin kirkiro sabbin abubuwa da kuma hanzarta mayar da tsoffin masana'antu zuwa na zamani. Bugu da kari, su tsaya kan ka'idojin yin hakuri da juna, da cimma moriyar juna domin kokarin neman bunkasa tare. Xi yana mai cewa,

"Ya kamata a fili kasashe daban daban su nuna adawa da manufofin kafa shinge ga cinikayyar da ake yi tsakanin kasa da kasa, da daukar matakai na kashin kai, ya kamata su yi kokarin bin manufar daidaita harkoki tsakanin bangarori daban daban, da daga matsayin bude kofofinsu, ta yadda za a iya ingiza yin mu'amalar tattalin arziki tsakaninsu, da kuma bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa. Bugu da kari, ya kamata kasashe daban daban su kara daidaita manufofi, da matakansu na bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa daga dukkan fannoni, domin rage matsalolin dake kawo musu illa. A waje daya, kamata ya yi a kafa wani sabon tsarin tattalin arziki da cinikayya cikin adalci, da gaskiya, ba tare da boye komai ba, ta yadda za a iya saukaka sharrudan yin cinikayya, da zuba jari da a kara bude kofa, da yin mu'amala, da hadin gwiwa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kasa."

Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40, tun bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida. A cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin tana cigaba da bude kofa ga waje. Ba ma kawai lamarin ya taimakawa kasar Sin kadai ba, har ma ya kawo alheri ga duk duniya. Bude kofa ga waje ya riga ya zama wata alama ta kasar Sin a zamanin yanzu. Shugaba Xi ya furta cewa, a shekaru 15 masu zuwa, kasarsa zata shigo da kayayyaki da darajarsu takai na dalar Amurka biliyan 30000, da ayyukan hidima masu darajar dala biliyan 10000, ka zalika Sin zata inganta bude kofa ga kasashen ketare ta fuskoki guda biyar, ciki har da inganta karfin shigo da kaya, da sassauta izinin zuba jari a Sin, da kafa muhallin cinikayya mai kyau kwarai a duniya, da habaka sabbin fannonin da za a bude kofarsu, da kuma inganta hadin kai daga bangarori da dama, da tsakanin bangarori biyu da dai sauransu. Game da yanayin kasuwancin da Sin ke ciki, Xi ya nuna cewa,

"kasar Sin zata kafa tsarin cin tara, ga wadanda suka karya dokokin kare ikon mallakar fasaha na halal na bakin 'yan kasuwa, sannan zata kara inganta aiki da saurin binciken ikon mallakar fasaha, domin kafa wani yanayin yin kasuwanci mafi kyau a nan kasar Sin."

Game da tattalin arzikin kasar Sin, Xi Jinping ya furta cewa, idan an kwatanta da sauran manyan kasashe a fannin tattalin arziki, kasar Sin tana sahun gaba a duniya ta fuskar karuwar tattalin arziki. Ya ce Sin tana da kyawawan yanayin kiyaye bunkasuwar tattalin arzikinta cikin dogon lokaci ba tare da tangarda ba. A ganinsa, tattalin arzikin kasar Sin tamkar wani teku ne maimakon tabki. Ko da guguwar iska ba zata kawo illa ga teku ba. Ya ce tabbas tattalin arzikin Sin zai kama hanyar neman samun bunkasuwa mai inganci yadda ya kamata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China