in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Bikin CIIE na zuwa! Duk duniya na kokarin neman shiga kasuwar kasar Sin
2018-11-04 17:46:24 cri

A gobe Litinin wato ranar 5 ga watan Nuwamba, a birnin Shanghai dake kasar Sin, za a kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko wato CIIE a takaice, wanda ya kasance irinsa na farko a duniya. Gwamnatin kasar Sin ce ta shirya bikin domin sa kaimi ga yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya wuri guda. A matsayinsa na wani sabon dandalin hadin kan kamfanoni fiye da 3000 daga kasashe da yankuna fiye da 130, bikin CIIE zai samar da sabuwar dama ga kasa da kasa wajen cin gajiya daga bunkasuwar kasar Sin.

Idan muka dubi duk duniya, za mu iya gano cewa, akwai bukukuwan baje-kolin kayayyakin shigi da fici iri daban daban. Amma bikin CIIE na wannan karo ya sha bamban sosai tare da su, wato bayan nune-nunen kayayyakin kamfanoni, za kuma a nuna kayayyakin kasashen duniya. Bayan cinikin hajoji da za'a yi, za kuma a yi cinikin ayyukan ba da hidima. Bugu da kari, ban da bikin nune-nunen, za a kuma tattauna kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayyar duk duniya.

Dalilin da ya sa bikin CIIE ya jawo hankalin mutane sosai shi ne saboda da farko da yana da girma, wanda murabba'in dakunan nune-nune ya kai murabba'in mita dubu 300. Ban da wannan, bikin ya samu halartar kasashe da yankuna fiye da 150, ciki har da kasashe mambobin kungiyar G20 da na kungiyar BRICS da na kungiyar SCO, da kasashe 58 da shawarar 'Ziri daya da Hanya daya' ta shafa, da ma kasashe mafiya fama da talauci guda 35. Bugu da kari, kamfanoni mahalartar bikin suna da inganci sosai, a cikin kamfanonin fiye da 3000, akwai kamfanoni fiye da 200 wadanda suke cikin jerin sunayen kamfanoni mafiya karfi 500 na duniya ko kuma wadanda suka yi matukar shahara a sana'o'insu. Haka zakila, za a nuna sabbin kayayyaki da fasahohin zamani fiye da 100 a yayin bikin. A sa'i daya kuma, taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa na Hongqiao wanda za a gudanar da yayin bikin, zai mai da hankali kan batutuwa uku, wato bude kofa ga waje, da kirkire-kirkire, da zuba jari, a kokarin bayar da gudummawar Sin ga ci gaban tattalin arzikin da cinikayyar duniya a halin yanzu.

A lokacin da ake yunkurin nuna adawa da bunkasar tattalin arzikin duk duniya baki daya, da ba da kariya ga cinikayya, sannan ake fuskantar matsin lambar raguwar saurin ci gaban tattalin arziki, masu tafiyar da masana'antu da 'yan kasuwa na kasashen duniya sun shiga damuwa sosai, dukkansu suna fatan za su iya mayar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wato wani sabon dandalin bude kofar kasar Sin, zama wata sabuwar damar sayar da kayayyakinsu a kasar. Kamfanoni wadanda suke samar da kayayyaki, da 'yan kasuwa wadanda suke cinikin waje suna mai da hankali sosai. A duniyar da muke ciki yanzu, ba a iya samun wata babbar kasuwar sayayya kamar kasar Sin wadda ke da mutane biliyan 1.4, ciki har da mutane miliyan dari 4 wadanda suke da matsakaitan rayuwa.

A cikin shekaru 40 da suka gabata bayan da aka kaddamar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje a kasar Sin, ba samun moriya sakamakon bude kofarta kadai ta yi ba, har ma tana tsayawa tsayin daka kan matsayin aiwatar da manufar bude kofa, a kullum ta tsaya kan manufofi da matakan yin cinikayya ba tare da shinge ba, da kuma saukaka yanayin zuba jari. A yayin wannan bikin baje kolin CIIE, baki 'yan kasuwa wadanda suka halarci bikin sun samu saukin shigar da kayayyakinsu kasar Sin, sannan bangaren Sin ya mai da hankali sosai wajen kare ikon fasaha da ba da hidimar hada-hadar kudi ga kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin. Sakamakon haka, an amince da cewa, dukkan baki 'yan kasuwa wadanda suka halarci bikin CIIE za su ji dadin matakan da kasar Sin ta dauka na kara bude kasuwanninta ga waje.

Kasar Sin ta kammala aikin kafa wani dandali, inda dukkan kasashen duniya za su iya more damammakin neman samun ci gaba. A cikin shekaru 5 masu zuwa, darajar kayayyakin da kasar Sin za ta shigo da su za ta kai dalar Amurka triliyan 8, tare da jarin waje dalar Amurka biliyan 600, sannan yawan jarin da za ta zuba a ketare zai kai dalar Amurka biliyan 750. A waje daya, kasar Sin za ta shirya irin wannan bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar kowace shekara, sabo da haka, bikin zai zama wani muhimmin dandali ga kamfanoni masu samarwa da kuma fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwar kasar Sin. Abin da ya fi muhimmanci shi ne, a kullum kasar Sin tana bayyana wa sauran kasashen duniya tunaninta na kokarin bude kofarta da yin hakuri da kuma moriyar juna domin cimma nasara tare da su. Wannan shi ne muhimmin jigo na tunanin raya wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama a lokacin da ake bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. (Sanusi Chen, Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China