in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CCTV ya taya murnar kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko
2018-11-04 16:10:17 cri

A yau Lahadi, an wallafa wani sharhi a shafin intanet na gidan talibijin na kasar Sin, wato CCTV a takaice, mai taken "Damar bunkasar kasashen duniya sakamakon ci gaban kasar Sin" wanda mai fashin baki na CCTV ya rubuta, domin taya murnar kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wato bikin CIIE a takaice.

A cikin wannan sharhi, an nuna cewa, za a kaddamar da bikin CIIE ne a birnin Shanghai a ranar 5 ga watan Nuwamba. Kamfanoni fiye da dubu 3 wadanda suka fito daga kasashe daban daban za su halarci bikin tare da kayayyakin da suke son shigowa kasar Sin. Sannan kusoshi da manyan 'yan kasuwa na kasashe da yankuna wajen 150 da shugabannin wasu kungiyoyin kasa da kasa su ma za su halarci bikin, inda za su tattauna da kuma tsara shirin neman ci gaba cikin hadin gwiwa. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne da kansa ya tsara ya kuma gabatar, tare da ingiza shawarar shirya bikin CIIE na farko. Bikin shi ne na farko, da za a baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wanda gwamnatin kolin kasar ta shirya a lokacin da kasar ke murnar cika shekaru 40 da kaddamar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. "Wannan ba baje koli irin na yau da kullum ba ne, wannan shi ke bayyana yadda muke jajijrcewa wajen daukar matakai da kanmu, na bude kasuwanninmu ga waje." Wannan muhimmin furuci na shugaba Xi Jinping ya kasance kamar wata babbar niyya da imanin kasar Sin na kara bude kofarta ga duk duniya a cikin sabon zamani. Kasar Sin wadda ta dauki matakan a zo a gani ta bayyana wa duk duniya cewa, ba za ta rufe kofarta da ta riga ta bude ba, sai dai ma ta kara bude ta a nan gaba.

Wannan sharhi ya nuna cewa, ba samun moriya sakamakon bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya kadai kasar Sin ta yi ba, har ma da bada gagarumar gudunmuwa ga ci gaban da aka samu. Tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri, sakamakon haka, yanzu ta kasance kamar wani "muhimmin inji" ko "anka" wajen bunkasar tattalin arzikin duniya. Sannan kasar Sin na kokarin fitar da salon cin nasara tare ta hanyar bude kofa cikin hadin gwiwa, kuma tana kokarin kafa tsarin tafiyar da duniya bisa adalci da gaskiya, sannan tana kokarin neman samun daidaito tsakanin kasa da kasa wajen bunkasa tattalin arzikinsu. Kasar Sin ta samu karfi daga sauran kasashen duniya wajen neman ci gaba, tana kuma kokarin amfana wa sauran kasashen duniya bisa ci gaban da ta samu. Shugaba Xi Jinping ya sha nanata cewa, "Da hannu bibbiyu al'ummar Sinawa ke maraba da al'ummomin kasashen duniya da su ci gajiyar kasar Sin kamar yadda za su shiga wani jirgin kasa mai saurin tafiya." Dalilin da ya sa aka shirya wannan gagarumin bikin gaje kolin shigowa da kayayyaki kasar Sin shi ne, bayyanawa duk duniya cewa, bisa matakin da kasar ta dauka, tana tsayawa kokarin yin cinikayya ba tare da shinge ba, da kara bude kofarta domin neman samun sabon ci gaba. Kasar Sin wadda ta samu ci gaba, wata dama ce ga sauran kasashen duniya. Fatan kasar Sin ita ce, sauran kasashen duniya su iya mayar da wannan biki zuwa wata dama, inda za su iya kara yin musayar ra'ayoyinsu da cimma matsaya daya, da ajiye sabaninsu a gefe, ta yadda za su iya cin moriya tare, da hada hannu wajen ciyar da tattalin arzikin duk duniya gaba, bisa ka'idojin kara bude kofa da hakuri da moriyar juna da neman daidaito tsakaninsu domin cimma nasara tare. Sannan za su iya hadin kai wajen kafa wata kyakkyawar duniyar dake da dawaumammen zaman lafiya da tsaron kai a ko ina da bunkasuwa, da amincewa juna tare kuma da tsabta. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China