in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanoni fiye da dubu daya na kasashe masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" sun halarci bikin CIIE
2018-11-03 20:08:56 cri
Bisa labarin da aka bayar a wurin taron manema labaru da aka yi game da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na farko wato CIIE, kamfanoni fiye da dubu daya na kasashe 58 masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" za su halarci bikin.

Mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Wang Bingnan ya bayyana cewa, bikin CIIE shi ne na farko da aka gudanar bisa taken shigar da kayayyaki duniya, wanda ya nuna goyon baya ga aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da sa kaimi ga samun ci gaba tare da moriyar juna a duniya. A shekaru 15 masu zuwa, kasar Sin za ta shigar da kayayyaki da darajarsu zai kai dala biliyan 24000, bikin CIIE zai samar da sabuwar dama ga kasashen duniya ciki har da kasashe masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya" wajen fadada fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin, da kafa sabon dandalin samun moriya tsakaninsu da kasar Sin, da kuma kara sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China