Shi ne kuma tauraron dan adam na farko mai juyawa lokaci guda da duniyar dan Adam, kana tauraron dan Adam na 41, a jerin taurarin dan-Adam samfurin Beidou na himdimar zirga-zirga.
Tsarin zirga-zirga na taurarin dan-Adam na Beidou, ba ma kawai zai iya samar da hidima mai inganci ga zirga-zirgar jiragen kasa, da na teku, da kuma motoci ba ne, har ma za a iya aika sako ta wannan tsarin ayyukan sa.
Kasar Sin ce da kanta, ta nazarta, da kuma kafa shi a sararin samaniya, yayin da ake sa ran tauraron zai rika aiki da kansa. (Sanusi Chen)