in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tauraron dan Adam mai aikin karba karba da zai yi aiki da na'urar Chang'e-4 ya shiga falakin sa
2018-06-14 20:13:09 cri
Tauraron dan Adam mai aikin karba karba, wanda zai yi aiki da na'urar binciken duniyar wata ta Chang'e-4 ya shiga falakin sa, na'urar kuma da ake sa ran za ta isa tsagin wata mafi nisa nan da karshen shekarar nan.

Hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin CNSA ce ta bayyana hakan a Alhamis din nan. Tauraron dan Adam din dai shi ne irin sa na farko a fannin ayyukan sadarwa da ke aiki a wannan falaki, zai kuma aza harsashin aikin da ake sa ran na'urar Chang'e-4 za ta gudanar, na'urar da ake fatan ita ce za ta kasancewa irin ta ta farko, da za ta sauka a wannan bangare na duniyar wata.

Da yake karin haske game da hakan, shugaban kwalejin nazarin ayyukan fasahohin sama jannati na kasar Sin Zhang Hongtai, ya ce yayin da tauraron ke sararin samaniya, zai iya hangen duniyar bil Adama, da kuma sashe mafi nisa na duniyar wata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China