A jiya Lahadi ne aka harba tagwayen taurarin dan Adam na kasar Sin samfurin BeiDou, ta hanyar amfani da rokar Long March-3B, daga tashar Xichang dake lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar ta Sin.
An harba taurarin biyu ne cikin nasara da karfe 10 saura mintuna 12 na safe, matakin da ya kasance na 281, a ayyukan harba kumbunan da aka yi amfani da rokar Long March wajen aiwatarwa.
Taurarin dan Adam din biyu, su ne na 33 da 34 a jerin taurarin BeiDou na kyautata tsarin sufuri. Sun kuma shiga falakin su bayan shafe sama da sa'o'i 4 da harba su.
Bayan gudanar da gwaje gwaje, ana sa ran za su yi aiki tare da wasu taurarin dan Adam 8 samfurin BeiDou-3 wadanda tuni ke sararin samaniya.
Ana sa ran nan da karshen shekara, za a sada taurarin dan Adam 18 samfurin BeiDou-3 dake sararin samaniya da na'urorin aiki, wadanda za su rika samarwa kasashen dake cikin shawarar nan da Sin ta gabatar ta "Ziri daya da hanya daya" hidimomi.