in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRI zai gabatar da shirye-shiryen bikin kaddamar da CIIE kai tsaye
2018-11-02 18:37:19 cri

Za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare na kasa da kasa ko CIIE karo na farko a birnin Shanghai, tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga wannan wata, inda manyan jami'ai, da wakilan masana'antu da kasuwanni, da kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa, wadanda suka zo daga kasashe da yankuna 150 za su halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu.

A safiyar ranar 5 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin kaddamar da bikin na CIIE, kuma zai gabatar da wani muhimmin jawabi, daga baya zai ziyarci dakin kasar da aka kebe, tare da manyan jami'ai na cikin kasar Sin da na kasashen waje.

Yayin bikin kaddamar da CIIE, gidan rediyon kasar Sin CRI zai gabatar da shirye-shirye kai tsaye da harsunan Turanci, da Japananci, da Jamusanci, da kuma yaren Indonesia. A sa'i daya kuma, zai gabatar da gajerun labarai game da bikin kai tsaye, da harsunan da yawansu zai kai 44, ciki hadda Hausa, da Turanci, da Japananci, da sauransu kan shafinmu na CRI Online, da dandalin sada zumunci na ketare da suka hada da Facebook da Twitter da VK da dai sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China