in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren IAEA: ana fatan fadada hadin gwiwa da bangaren Sin
2018-11-02 13:59:12 cri
Mr. Yukiya Amano, babban sakataren hukumar makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana cewa, yana fatan fadada hadin gwiwa tsakanin hukumarsa da bangaren Sin a fannoni daban daban.

Mr. Yukiya Amano ya bayyana haka ne a jiya Alhamis, yayin da yake ganawa da wakilin kasar Sin Wang Qun dake hukumomin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Vienna, inda ya kuma yaba da ci gaban da kasar Sin ta samu wajen amfani da makamashin nukiliya, da gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen tabbatar da tsaron nukiliya a duk duniya. Bugu da kari, ya yabawa rawa da tasirin kasar Sin kan batutuwan nukiliyar yankin Koriya da na kasar Iran.

A nasa bangaren, Mr. Wang Qun ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin da hukumar IAEA sun yi cikakkiyar hadin gwiwa a fannonin yin amfani da makamashin nukiliya da tabbatar da tsaron nukiliya da yin amfani da fasahohin da ke shafar nukiliya da dai makamatansu, kuma sun samu sakamako mai tarin yawa. Mr. Wang ya kara da cewa, kasar Sin na fatan kara yin kokari tare da babban sakataren da kuma hukumarsa wajen tabbatar da cimma burin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana da kuma burin hana yaduwar nukiliya domin kafa wani kyakkyawan yanayi mai tsabta. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China