Babban darektan hukumar IAEA, Yukiya Amano, ya gabatar da rahoton aikinsa ga kwamitin zartaswar, inda ya maida hankali sosai kan tsaron makamashin nukiliya a fadin duniya.
Mista Yukiya Amano ya bayyana cewa, an yi shekaru kusan shida da aukuwar hadarin tashar samar da wutar lantarki bisa karfin makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi a kasar Japan, lamarin da ke kashedin cewa, ya zama dole a ci gaba da inganta tsaron makamashin nukiliyar a fadin duniya.
Taron IAEA da aka bude a wannan karo, zai kara nuna kwazo a fannonin da suka shafi batun makamashin nukiliya, da burbushin nukiliya, tare kuma da yin jigilar makamashin.(Murtala Zhang)